Matasa masu goyon shirin karba-karba sun gwabza da ‘yansanda a Bauchi

  • Aliyu Mustapha
Matasa masu goyon bayan shirin karba-karba sun ce ‘yansanda na takura musu ‘yancinsu na walwala da bayyana ra’ayinsu kan shirin karba-karba.

Zirga-zirga da harakokin kasuwanci sun tsaya cik jiya a Bauchi, musamman kan titunan dake zuwa kasuwar Muda Lawal, a sanadin zo-mu-gaman da akayi tsakanin ‘yansanda da gungun wasu matasan ci-gaban Arewa masu goyon bayan shirin karba-karba. Shugaban kungiyar, Halilu Ladan ya zargi ‘yansanda da cewa suna danne musu hakki, kuma suna kare gwamnati. Yace sun nemi iznin suyi wannan zanga-zangar nunin goyon baya ga shirin karba-karba din, amma ‘yansandan suka hana su. Shugaban matasan yace sun sanarda dukkan hukumomin tsaro da na gwamnati da suka kamata, irinsu su ‘yansanda da SSS da sojoji akan cewa zasuyi wannan gangamin, amma duk da haka ba’a barfsu suka yi shi ba. Matasan suka ce duk da yunkurin hana su yin gangamin, ba zasu fasa ba. To amma kakakin ‘yansanda Walter Eyang, wanda ya jagoranci ‘yansandan da suka hana wa matasan yin zanga-zangar, yace sun yardar wa matasan suyi taronsu a dandalin IBB Square dake nan Bauchi amma sai matasan suka nemi zarcewa zuwa gidan gwamnati, wanda su kuma ‘yansandan suka ce basu yarda ba.