Batutuwan Da Shugaba Isuhu Na Nijar Ya Tabo a Jawabin Sabuwar Shekara

Shugaban Jamhuriyar Nijar, Muhamadu Isuhu

Yayin da aka shiga sabuwar shekara shugaban kasar Nijar Muhamadu Isuhu ya kudiri anniyar bude wasu sabbin barikin sojoji don karfafawa dakarun  kasar gwuiwa a shekarar ta 2018.

Shugaban Jamhuriyar Nijar, Muhamadu Isuhu ya bayyana aniyarsa ta gina sabbin barikin sojoji a kasar a wani mataki na kara kaimi wajen yaki da ayyukan ta’addanci.

Shugaba Isuhu ya bayyana hakan ne yayin jawabin da ya yi wa ‘yan kasar na murnar shiga sabuwar shekara.

Shugaban ya ce dalilin haka ne gwamnatinsa ta ware kashi 15 cikin 100 na kasafin kudin kasar a matsayin kudaden da za a yi amfani da su wajen sayen kayayyakin aiki.

Isuhu har ila yau jinjina wa dakarun kasar da suka rasa rayukansu a filin daga, sannan ya tabo batutuwan da suka shafi sauyin yanayi da gina kasa a matsayin wasu matsalolin da ke zama kalubale ga kasar.

Sai dai wasu masu fafutuka na korafi kan yadda shugaban ya manta da wani muhimmin batu da ya faru a yankin jihar Diffa mai fama da matsalar tsaro.

“Iyali gaba daya a ka zo aka kwashe mutum 39, ka ga ba abu bane da ya kamata a manta da su, ya kamata a ce yana kwana da tashi da wannan batun. Ya kamata a dauki matakan da za a gane suna da rai ko sun mutu.” Inji Alhaji Salissou Amadou na gamayyara kungiyoyin masu fafutukar kare hakkin bil adama.

Saurari rahoton Sule Mumuni Barma domin jin karin bayani:

Your browser doesn’t support HTML5

Batutuwan Da Shugaba Isuhu Na Nijar Ya Tabo a Jawabin Sabuwar Shekara - 2'58"