Batun Tsige Trump Ya Fara Daukar Zafi

Shugaba Donald Trump

Wasu muhimman mutane a shari’ar tsige shugaban Amurka Donald Trump da masu kare shi, sun yi musayar yawu mai zafi a jiya Lahadi a kan yunkurin da ya yi na tursasa Ukraine ta gudanar da binciken da zai taimaka masa a siyasance da ya kai ga tsige shi daga ofishi.

An dai bude shari’ar da ake yiwa Trump a Majalisar Dattawa a hukumance ne a karshen makon jiya yayin da za a fara gabatar da hujjojin yanke hukunci a gobe Talata.

Amma masu cacar baki ta fannin siyasa da doka a kan makomar Trump a wannnan batu, sun yi musayar yawu a kafafen yada labarai da safiyar jiya Lahadi a fadin Amurka, lamarin dake nuna irin dambarwar da Amurkawa za su gani a Majalisar Dattawa.

Wani lauyan kare masu laifi, kuma daya a cikin rukunin lauyoyi masu kare Trump Alan Dershgowitz ya fadawa shirin CNN na State of the Union cewa zai fadawa ‘yan Majalisar Dattawa guda dari da zasu yi shari’a a kan makomar Trump cewa, koda bayanan da aka gabatar musu gaskiya ne, laifin bai kai a tsige shi daga ofis ba.

‘Yan Majalisar dai sune za su yanke hukunci a kan ko Trump ya aikata manya ko kananan laifuka da suka sabawa tsarin kudin mulkin Amurka da zai kai ga tsige shugaban kasa.