Batun Tsaro Da Tattalin Arziki Jama'a Su Ka Fi Tattaunawa Kan Mulkin Buhari Na Shekaru 8

Bayanan jama’a

Batun tabarbarewar tsaro da kuma kuncin tattalin arziki su ka fi zama abubuwan tattaunawa a tsakanin ‘yan Najeriya musamman talakawa kan mulkin shugaba Buhari na shekaru 8.

Da alamar mutane kan yi magana a kan wadannan al’amura don su na cikin abubuwan da shugaban ya yi alkawarin gyarawa in ya dare kujerar shugaban kasa.

Irin bayanan jama’a kenan da wasunsu duk da kalubalen da a ke fuskanta kan ce a yi fatan alheri ko addu’a don samun sauki.

Ga Farfesa Usman Yusuf da kan ba da gudunmawa ga lamuran tsaro, ya zama mai muhimmanci a nazarci asalin abubuwan da su ka haddasa rashin tsaron da ya addabi wasu jihohin arewa maso yamma.

Fred Manjack tsohon ma’aikaci ne a ma’aikatar labaru wanda ke da lalurar kafa kuma ya jajirce har ya yi ritaya, ya nuna korafin rashin samun kulawa ta musamman ga mutane irinsa ba kamar ma wadanda ko aikin ba su da damar yi ba.

A wata amsa da ya bayar kan tsaro da ma kuncin rayuwa, mai taimaka wa shugaba Buhari kan labaru Garba Shehu ya ce shugaba Buhari ya yi tsayin daka wajen rike amanar kasa don haka jama’a ya dace kowa ya rika ba da hadin kai don samun cikakkiyar nasara.

Wani sauyi a nan a karshen gwamnatin Buhari shi ne rage dora matsalolin kasar kan tsohuwar gwamnatin PDP inda gwamnatin ta APC kan ce ta ware makudan kudi a kowane bangare don kawo gyarar da ta yi alkawari.

Saurari rahoton Hauwa Umar:

Your browser doesn’t support HTML5

Batun Tsaro Da Tattalin Arziki Su Ka Zama Abun Tattaunawar Jama’a Kan Mulkin Buhari Na Shekaru 8