Batun Tsarin Iyali Da Hakkin ‘Yan Mata: Sarakuna, Shugabannin Addinai Da Hukumomin Nijer Na Taro

Wani taron sarakuna a Nijer

Batutuwan tsarin iyali da kare hakkin ‘yan mata sun janyo taron Sarakunan gargajiya da shugabanin addinai a bangare guda, da kuma hukumomin kasar da hukumar UNFPA a daya bangaren da nufin tattaunawa.

Babban makasudun wannan taro da ake kira Symposium des Chefs traditionnels shi ne nazari akan matsalolin da ke mayar da hannun agogo baya wajen ganar da al’umar wannan kasa muhimmancin tsarin iyali bayan shafe shekaru ana yi wa wannan batu mummunar fahimta sakamakon mummunar fassarar da aka yi wa abin tun a tashin farko, kamar yadda Cheick Tidinae N’diaye jami’i a hukumar MDD mai kula da harakokin al’umma (UNFPA) ya bayyana ma Muryar Amurka.

Batun ilimin ‘yan mata na daga cikin batutuwan da za a yi nazari kansu a wannan zama don ganin an bullo da wasu hanyoyin kawo karshen dabi’ar nan ta auren wuri da auren dole wadanda ke zama dabaibayi ga karatun ‘yan mata.

Sarakunan gargajiya na kan gaba a wannan yunkuri, kasancewarsu shuwagabanni mafi kusa da al’umma kuma masu bakin fada a ji. Sarkin Damagaram mai martaba sultan Aboubacar Sanda Oumarou ya bayyana muhimmancin wannan haduwa ga ci gaban al’umma.

Rashin bai wa ‘yan mata damar gwada sa’arsu a makarantun boko saboda dalilai masu nasaba da al’adu ko addini wani abu ne da ake ganinsa tamkar wani tarnaki ga ci gaban al’umma saboda haka matasa ke ganin bukatar daukar tsauraran matakan da za su haramtar da dabi’un da ake ganin su na jefa ‘yan mata cikin mawuyacin hali.

Malaman addinai sun yi amannar cewa halin da ake ciki a yau na bukatar gyara amma kuma ya kasance ana sara ana dubin bakin gatari. Daga cikin masu wannan ra’ayin akwai Malan Sabi Souleymane da ke shugabancin wata kungiyar addinin islama.

Kwanaki 2 za a shafe ana gudanar da wannan taro wanda a karshe zai bullo da wasu muhimman shawarwari kuma shugaban kasa Mohamed Bazoum wanda ya jagoranci bukin bude wannan zama ya shawarci sarakuna su kuduri aniyar ganin cewa daga yanzu ba wanda zai sake aurar yarinyar da ba ta kosa ba, ta yadda talakawa za su yi koyi da su akan wannan magana ta kare yara kanana daga matsalolin dake tattare da auren dole da auren wuri.

Saurari rahoton Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Taron Sarakunan Gargajiya a Nijer