Fadar White House, ta nuna alamun a shirye take ta sake shiga tattaunawa da ‘yan jam'iyyar adawa ta Democrats akan tallafin coronavirus, kuma za ta yadda a kashe karin kudi don su cimma matsaya.
WASHINGTON D.C. —
“A shirye muke mu sake gabatar da batun karin kudi a teburin tattaunawa” a cewar Sakataren Kudi Steven Mnuchin da yake magana a gidan talabijin na CNBC.
Ya kuma ce “shugaban kasar a shirye yake ya kashe abunda ake bukata”.
Shugaba Trump ya rattaba hannu akan dokar da ya kafa da ikonsa na shugaban kasa ran Asabar don dada bai wa miliyoyin wadanda suka rasa aiki tallafin da wa'adin bayarwa ya kare, da kuma jinkirta haraji ga Amurkawa ma’aikata.
A wani sabon bayani da yayi a shafinsa na Twitter, Trump bai kau da yiwuwar sake tattaunawa ba, amma ya zargi shugaban ‘yan democrats, Chuck Schumer da shugabar majalisar wakilai, Nancy Pelosi da janyo rashin cimma matsaya a tataunawar na ran asabar.