Batun Akwai Siyasa Domin an Gargadesu da Kada su Zabe Jamiyyar APC

Gwamna Jihar Gombe Ibrahim Dankwambo.

A Jihar Gombe masu rike da sarautun gargajiya goma sha shida ne aka dakatar dasu da daga kan mukaminsu a karamar hukumar Akko da suka hada da Hakimai guda hudu da kuma Dagatai guda goma sha biyu.

Hukumomin karamar hukumar sun bada bayanin cewar dakatarwan ya biyo bayan laifin rashin girmama hukuma da kuma kin bin ka’idar aiki ne dalilin dakatarwan.

Su kuma masu sarautun na cewa batun akwai siyasa a cikin domin an gargadesu da kada sun zabe jamiyyar APC, ta adawa.

Mataimakin shugaban karamar hukumar Akko,Muhammad Ibrahim Jalo, yayi bayani a hukumance yana cewa sun dai Hakiman da Dagatai ma’akatan karamar hukumar Akko, ne wanda kuma shi shugaban karamar hukumar Akko, ya bada sanarwar dakatar dasu, aka kuma kafa kwamiti don bin ba’asin abun da ake zargin su dashi na rashin yiwa hukuma biyayya da kuma rashin bin ka’idodin masarauta, wannan sune dalilai.