Bashin Ya Isa Haka Buhari - 'Yan Najeriya

shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mikawa majalisar dattawan kasar wata wasika domin su bashi dama ya karbo bashin kusan dala biliyan talatin ($30B) daga kasashen waje.

Wasu ‘yan Najeriya na ci gaba da bayyana ra’ayoyin su akan bukatar da shugaban kasar na karbo bashin, bayan wanda ke akwai a halin yanzu.

Dayawa daga cikin wadanda suka bayyana ra’ayin su sun ce basu ga amfanin karbo bashin ba, saboda har yanzu basu gani a kasa ba na irin makudan kudaden da aka karbo daga kasashen waje.

A cikin wata wasika wasu kungiyoyi sama da talatin masu zaman kan su da ke gwagwarmayar wanzar da shugabanci na gari a Najeriya sun bayyana matsayar su cewa basa goyon bayan karbo wannan bashi da suke ganin zai zamarwa kasar wani karfen kafa.

"Yanzu haka bashin da yake kan Najeriya ya yi yawa sosai, wanda kasar take biyan kusan fiye da kashi hamshin na kudaden shiga da take samu wajan biyan bashin da yake kanta", a cewar jagoran kungiyar CISLAC da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Shi ma wani mai fashin baki akan harkokin siyasa da tattalin arziki ya ce ya kamata ayi taka tsantsan da ciyo bashi, idan aka yi la’akari da irin bukatun kasar na manyan ayyuka.

Sai dai a lokacin da Sanata Bukola Saraki ya ke shugabancin majalisar dattawan kasar ta takwas da ta gabata, shugaban Buhari ya taba mika wannan bukata da suka ki amincewa da ita.

Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari daga Kano:

Your browser doesn’t support HTML5

Bashin Ya Isa Haka Buhari - Yan Najeriya