Bashi Ya Kusa Durkusar da Wani Banki

Dr. Babangida Aliyu gwamnan jihar Neja.

Makon da ya gabata rahoto daga jihar Neja yace wasu sun yi sama da fadi da kudin wani karamin banki.

Biyo bayan rahoton da Muryar Amurka ta dauka akan karamin banki dake da suna Tattali Microfinance Bank, yanzu jami'an bankin sun fito da bayanin abun da ya addabi bankin.

Daya daga cikin daraktocin bankin Alhaji Muhammad Kudu yace masu karbar bashi a bankin ne suka nemi durkusar dashi. Ma'ana suna cin bashi amma basa biya. Amma yace yanzu an shawo kan lamarin. Yace ba wai wasu ne suka sace kudin bankin ba. Wadanda suka ci bashi ne basu biya ba. Ban da haka jami'an dake gudanar da harkokin bankin sun bayar da bashi fiye da ikonsu. Su wadannan an koresu kuma an kawo wasu sabbin shugabannin bankin. Ana zaton zai fara aiki mako mai zuwa.

Da yake magana akan wadanda suke da ajiya a bankin Alhaji Muhammad Kudu yace an bi duk kaidodin bude bankin kuma koda ya durkushe inshora za ta biya kowa abun da ya ajiye a bankin.

Babban daraktan ma'aikatar dake kula da kananan bankuna a jihar Neja Malam Bako Muhammad Bawa yace sun yi kokarin shawo matsalolin da suka addabi kananan bankuna. Sabo da haka ya shawarci jama'a su kwantar da hankalinsu. Yace babu matsala da kananan bankunan dake jihar. Masu matsalolin an dauki matakai kuma an warwaresu.

Masu hulda da bankin sun ce suna addu'a a bude domin suna wahala. Sun ce a karamar hukumar Mashegu bankin shi ne kadai daya tilo da suke dashi.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.

Your browser doesn’t support HTML5

Bashi Ya Kusa Durkusar da Wani Banki - 2' 26"