Kungiyar Bayern Munich ta ragargaza Barca din ne da zunzurutun ci 8-2, a wasan quarter-final ta gasar zakarun Turai, kashi mafi muni da kungiyar ta taba sha a tarihi.
Yanzu haka kungiyar ta saka kusan dukan ‘yan wasanta a kasuwa, bayan da ta ce ta lura akasarinsu sun soma tsufa, yayin da kuma tauraruwarsu ke kara disashewa.
Wata jaridar wasanni ta 'Mirrow' ta ruwaito cewa shugaban kungiyar Josep Maria Bartomeu, na shirin yin shara da garambawul a kungiyar, tare da maye gurbin da ‘yan wasa sabbin jini, to amma zaratan ‘yan wasa da suka hada da Lionel Messi, Marc-Andre ter Stegen, Clement Lenglet, da Frenkie de Jong, ba sa cikin guguwar barin kungiyar.
Haka kuma kungiyar ta sabunta fafutukar dawo da tsohon dan wasanta Neymar da ya koma PSG ta kasar Faransa, inda yanzu haka ta shirya biyan kudi da bayar da wani dan wasa domin dawo da Neymar.
Rahotanni sun bayyana cewa Barca din ta shirya biyan kudi fam miliyan 54 da kuma dan wasanta Antonie Griezman akan tsohon dan wasan na ta da ta sayar a kan farashi mafi tsada a duniya na fam miliyan 200 a shekara ta 2017.
Neymar mai shekaru 28, ya kwashe tsawon shekaru 3 a Barcelona, inda ya zura mata kwallaye 105 a cikin wasanni 186 da ya buga mata, ya kuma taimaka mata ta lashe gasannin La Liga da zakarun turai.
Haka kuma kungiyar na nan tana aikin nemo sabon mai horar da ‘yan wasanta, inda wasu rahotanni suka ce ta soma tattaunawa da kocin kasar Holland, Ronald Koeman domin ya maye gurbin Quique Setien.