Kungiyar kwallon kafar Barcelona sun fara kwallon kakar nan karkashin sabon manaja Luis Enrique, amma saidai a kwai alamun tambaya ga sabon manajan din tunda kungiyar bata sami nasarar cin wasaba a wasannin kusa kusa nan da sukayi na La Liga, kuma sun gaza yin wasan da ake tsammaninsu da yi.
Abin mamakine shine ganin kungiyar wasa ta El Clasico ta baiwa Bercelona kashi a wasan da sukayi satin daya wuce biyo bayan dan Karen kashi da Real Madrid ta baiwa Barcelona.
Kungiyar kwallon ta Barcelona dai sun rasa damar cin mayan kofiffika a kakar bara da data wuce, wanda ya kawo karshen Gerardo Martino daga kungiyar, amma da akwai dan abubuwan dake nuna wa cewa za’a samu cigaba, saboda akwai sabbin hanyoyin da za’a iya gwadawa cikin wasan.