Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Tsallake Rijiya Da Baya A Fagen Kwallon Kafa


Supporters of Nigeria's football team celebrate their 2 - 1 victory over Ethiopia in their 2014 World Cup qualifying match.
Supporters of Nigeria's football team celebrate their 2 - 1 victory over Ethiopia in their 2014 World Cup qualifying match.

Najeriya ta sake kaucewa shiga tarkon hana mata buga kwallon kafa na kasa da kasa har na tsawon watanni 7 da hukumar FIFA ta shirya, a bayan da wata babbar kotun tarayya dake Jos ta soke karar da aka shigar kan halalcin zaben shugabannin hukumar kwallon kafa ta Najeriya.

A watan Satumba ne wakilan hukumar suka yi watsi da wani haramcin kotu suka gudanar da zabe a garin Warri inda aka zabi Amaju Pinnick a zaman shugaba.

Shugabannin da aka ce an zaba kafin nan kuwa, karkashin jagorancin Chris Giwa, sun shigar da kara a kotu sun a kalubalantar zaben na Pinnick.

Amma a yau alhamis, bangaren Chris Giwa sun janye karar da suka shigar din, a dalilin abinda lauyansu Habila Ardzard ya bayyana a zaman rook daga ‘yan Najeriya kuma domin kare muradun kasa.

Yau watanni 4 ke nan da hukumar NFF ta tsunduma cikin rikicin shugabanci, kama daga watan Yuli a lokacin da wata kotu a Jos ta rushe hukumar karkashin jagorancin Aminu Maigari. Ministan wasanni ya nada wani ma’aikaci ya jagoranci hukumar, abinda ya fusata hukumar FIFA har ta dakatar da Najeriya.

A wannan karon, hukumar ta FIFA ta ba Najeriya wa’adin zuwa gobe Jumma’a ne kan ta tabbatar da Pinnick a kan kujerarsa ko kuma Najeriya ta yi bai-bai da wasannin kasa da kasa har na stawon akalla watanni 7.

XS
SM
MD
LG