Barbara Bush Uwargidan Tsohon Shugaban Amurka George H.W.Bush Ta Rasu Tana Da Shekaru 92

Barbara Bush, uwargidan tsohon shugaban Amurka George H.W. Bush

Allah ya yiwa Barbra Bush matar tsohon shugaban Amurka George H. W. Bush har wayau kuma uwar tsohon wani shugaban na Amurka George W. Bush jiya da maraice a gidansu dake Dallas cikin jihar Texas

Barbara Bush, urwagidan tsohon shugaban Amurka, George H.W. Bush ta rasu, tana mai shekaru 92.

Wata sanarwa da iyalan marigayiyar suka fitar a jiya Talata, ta bayyana cewa, Barbara, ta rasu ne da yammacin jiya Talata, zagaye da iyalanta.

“Mahaifiyata ta rasu tana mai shekaru 92,” Tsohon shugaban Amurka, George W. Bush, wanda da ne ga marigayiyar ya fada a sanarwar.

Iyalan na Bush ba su ba da cikakken bayani kan rashin lafiyarta ba, amma a ‘yan shekarun baya, Barbara Bush ta sha fama da matsalar cutar zuciya da ta numfashi.

Ta kuma ki amincewa ta ci gaba da neman magani a ‘yan shekarun nan da suka gabata, bayan da lafiyarta ta yi ta tabarbarewa.

Barbara, mata ce da aka santa wajen kare mijinta da ‘ya’yanta

Marigayiyar da mijinta Bush babba, suna da yara shida, ita ce uwargidan shugaban Amurka ta biyu da mijinta ya taba shugabantar Amurkan, sannan danta ma ya yi shugabancin kasar, baya ga Abigail Adams, uwargidan tsohon shugaba John Adams, wanda shi ne shugaban Amurka na biyu, wacce har ila yau danta John Quincy Adams shi ma ya mulki Amurka a matsayin shugaban kasar na shida.