Kafafen yada labaran Amurka sun ce fargaban harin Bom daga ‘yan kungiyar ISIS ya sa hukumomin Amurka fidda dokar hana pasinjoji daukar manyan na’urori masu amfani da lantarki a wuraren da suke zama daga tashoshin jiragen saman wasu kasashen gabas ta tsakiya.
Jaridar New York Times ta amabaci wata majiya da bata bayyana ba, na cewa an yi dokar ne don dakile shirin mayakan ISIS na kera dan karamin Bom wanda za a iya boyewa a cikin batirin kwamfutar tafi-da-gidanka.
Gidan talabijin din ABC ya bada rahoton cewa bayanan sirri da jami’an Amurka suka samu a farkon watan nan sun nuna cewa ‘yan ISIS na kokarin samun hanyar shigowa da ababen fashewa (nakiyoyi) cikin jiragen da zasu zo Amurka. Wata majiyar gwamnati ta fadawa gidan talabijin din na ABC cewa bayanin barazanar na da tushe kuma akwai kamshin gasikiya a cikin sa.