Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsayar Gwamnatin Donald Trump A Kan Tatsar Bayanai


Jiya Talata da kyar 'yan Republican suka amsa cewa akwai abin da Ciyaman din Kwamitin Majalisar Wakilai Kan bayanan Sirri, Devin Nunes, ya bayyana da "wata babbar ayar tambaya" game da makomar gwamnati mai ci, bayan da Shugaban hukumar bincike ta FBI James Comey.

Jami'in ya bayyana cewa hukumar tasa na binciken yiwuwar alaka tsakanin Kwamitin yakin neman zaben Trump, da kasar Rasha.

Haka zalika, a zaman Majalisar da ta gabata, da kyar 'yan Majalisar Wakilai na jam'iyyar Republican, su ka ambaci fitowa karara da Comey ya yi, na yin watsi da zargin da Trump, ya yi cewa tsohon Shugaban Barack Obama ya yi ta tatsar bayanai game da shi a yayin zaben 2016.

Haka kuma sun ki cewa wani abu akai ko a yayin da su ka tashi daga wata ganawa da Shugaba Donald Trump, wanda ke kokarin zawarcinsu don samun isasshen kuri'u na amincewa da sabon kudurin doka na shafewa da kuma maye gurbin Dokar Saukake ma majinyaci samun lafiya wadda aka fi sani da Obamacare.

"Da gaske ka ke yi kuwa?" abinda dan Majalisar Wakilai Walter Jones, dan jam'iyyar Republican daga North Carolina, ya fada kenan bayan da aka tambaye shi ko shin Shugaban kasa ya tabo batun zargin na tatsar bayanai a yayin ganawarsu gabanin kuri'ar da za a kada kan saukaka jinya din ranar Alhamis.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG