Duk da kokarin kutsawa dajin da 'yan-bindiga ke buya da jami'an tsaron Najeriya ke yi a wasu sassan Kaduna da Filato, al-ummar yankin Birnin Gwari sun ce suna cikin barazanar 'yan-bindiga masamman ma ga manoman yankin.
Tun farkon damunar bana dai 'yan-bindigan yankin Birnin Gwari suka aikawa da manoma bukatar zaman sulhu kafin su yi noma, sai dai kuma shugaban kungiyar al'ummar Birnin-Gwari Malam Ishaq Usman Kasai, ya ce har yanzu manoman yankin na cikin wani hali.
Maganar matsalar tsaro a yankin Birnin-Gwari dai na cikin manyan matsalolin da masana harkokin tsaro ke ganin akwai bukatar sauya salo.
Ku Duba Wannan Ma RASHIN TSARO: Noma Na Ci Gaba Da Gagara A Yankin Birnin Gwari
Duk da rashin tabbas na sulhu da manoma kan yi da 'yan-bindiga dai, wasu manoman yankin sun riga sun yi wannan sulhu, sai dai kuma shugaban kungiyar al'ummar Birnin-Gwarin, Malam Ishaq Usman Kasai ya ce sulhun bai haifar da da mai ido ba.
Barazanar 'yan-bindiga dai na cikin jerin matsalolin tsaron da wasu ke ganin ka iya haifar da yunwa da karancin abinci idan ba mahukunta sun gaggauta daukar matakai ba.
Saurari rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5