Barazanar Rufe Ma'aikatun Amurka

Akwai fargabar daya bisa hudu na ayyukan gwamnatin Amurka zai tsaya cik daga karfe 12 na daren ranar Jumma’a da ke tafe, muddin fadar shugaban kasar ta White House da ‘yan Majalisar Dokokin Tarayyar Amurka su ka kasa cimma jituwa kan sabon kasafin kudi.

Daga cikin takaddamar har da zancen gina katanga tsakanin Amurka da Mexico, kamar yadda Shugaba Donald Trump ke so, don dakile kwararowar bakin haure.

Tuni dai aka amince da kasafin kudin gudanar da rubu’i uku na ayyukan gwamnati zuwa watan Satumba mai zuwa.

Amma sauran kasafin kudin ya hada har da na tafiyar da harkokin Ma’aikatar Tsaron Gida, mai yiwuwa kuma har da kudin gina katanga, wanda wani muhimmin alkawari ne na yakin neman zabe da Trump ya yi a lokacin yakin neman zabe a 2016.

Amma dala biliyan 5 din da Trump ke bukata daga jimillar dala biliyan 20 na gina katanga, na samun matukar turjiya daga ‘yan Democrats da wasu ‘yan Republican, wanda ke haifar da shakku kan yiwuwar gina katangar.

‘Yan Democrats sun yi tayin abin da ba zai wuce dala biliyan 1.6 ba, saboda inganta tsaron kan iyaka; ko shi din ma, ba don gina katanga ba.