A cikin hirarsu da Sashen Hausa, Dr Mustapha Muktar yace,wannan matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na umartan gwamnatocin jihohi da ma’aikatun gwamnmatin tarayya su rika ajiye kudinsu a banki daya suna da alfano ta fannoni da dama. Na farko idan aka dubi kudaden gwamnati da suke yoyewa idan an karba kasancewa a da ana bude ajiya ne a bankunan kasuwanci da yawa, wani lokaci sai kudin ya yoye baije hannun gwamnati ba wannan zai sa aci amfanin kudin.
Yace wannan zai rage cin hanci da rashawa, banda haka kuma zai karawa gwamnati karfin guiwa ta iya gudanar da wadansu ayyuka da take gaza aiwatarwa sabili da kudaden basu shiga.
A bangaren cibiyoyin kasuwancin kuma Dr Murktar yace yanzu bankunan dake dogaro ga irin wannan ajiyar zasu tashi tsaye domin su nemi wadansu hanyoyin da zasu rayu. Yace ko da yake da farko zai iya zama babbar kalubala ga bankunan da ya yiwu da dama su nemi zaftare ma’aikata, amma daga baya zasu mike su rika gudanar da ayyuka yadda ya kamata bankunan kasuwanci su yi.
Cikakkiyar hirarsu da Mahmud Lalo
Your browser doesn’t support HTML5