Bankuna Sun Fara Shiga Masana'antar Kannywood

Murtala Balarabe Baharu

Shirin nishadi na yau, ya karbi bakoncin jami’i mai hulda da jama’a na kungiyar MOPPAN Murtala Balarabe Baharu, wanda ya ziyarci DandalinVOA inda ya ke sheda cewar masana'antar Kannywood zata farfado da karfinta, da cewar Bankin 'yan kasuwa zai ba masana'antar lamuni domin inganta sana’ar.

Bankin zai bada lamunin ne, ganin yadda masana'antar matsaloli suka yi mata dabaibayi na rashin kasuwa, rashin gudanar da harkar fim yadda ya kamata, uwa uba rashin kasuwar da masana'antar ke fuskanta a yanzu.

Ya kara da cewa wannan lamuni zai farfado da masana’antar tare da dawo da martabar Kannywood, inda yake cewa shirin zai samar da ilimin harkar fim, gwamantin jihar Kano da Bankin masana'antu sun amince da tsayawa wajen bada naira miliyan duba daya wajen wannan shiri.

Bankin dai zai bada naira miliyan daya ne ga kamfanonin da suke da katin CAC wato rijistan kamfani, da kuma cikakkun bayanai na yadda zasu gudanar da wannan aiki na fim da Bankin zai ba da tallafi.

Amma fa wanda zasu sami wannan tallafi lallai sai wadanda suke cikin masana'antar Kannywood, walau mai shiryawa ko marubuci da sauransu.

Kawo yanzu dai tuni aka kafa kwamitin da zai lura da wadannan ka’idoji na karba da shirya fina-finai ta hanyar karbar wannan lamuni.

A yanzu dai an bada tsawon mako biyu domin cikin guraben na cike dukkanin ka'idojin da za’a bi kafin a samu wannan tallafi.

Your browser doesn’t support HTML5

Bankuna Sun Fara Shiga Masana'antar Kannywood 5'40"