Bankin Masana'antu Ba Zai Yafewa Masu Burodin Rogo Bashin Biliyan Uku Da Rabi Ba

Naira

Bankin raya masana’antun Najeriya ya nuna rashin amincewa da bukatar masu gasa burodin rogo, ya yafe bashin da su ka karba na Naira biliyan 3.4 don bunkasa wannan sana’a.

Lamunin dake samarda da fulawar rogo da kamfanonin burodi ke amfani da shi, ya faro ne daga shekara ta 2008, lokacin da gwamnatin Najeriya ke son fadada masana’antun sarrafa kayan noma na Najeriya.

A taro kungiyar masu gasa burodin rogon a Abuja, daraktan sashen hana asara na bankin Dr.Ezekiel Oseni, yace gwamnati ba za ta yafe bashin hakanan ba, domin kamfanoni 5 ma sun rufe aiki ba tare da biyan bashin ba.

Oseni yace duk sana’a ta na da kaddarar samun asara, amma ba za a goge bashin ba, don hakan zai hana gwamnati samun damar ba wa wasu ‘yan kasuwar lamunin.

A zantawa da gidan talabijin na BEN AFRICA, shugaban bankin Olukayode Pitan ya fadi dalilan da a ke ganin, su suka sa mutane kasa dawo da lamunin.

Alhaji Adamu Hassan na kungiyar ‘yan kasuwar arewacin Najeriya wanda su ka yi ta gwagwarmayar neman lamunin bankin masana’antun ba su samu ba, yace rashin nazarin inda bankin zai ba da lamunin ne ya jawo rashin biyan.

Bankin na tallafawa masana’antu na da tsarin irin sauran cibiyoyin gwamnati da ba sa samar da riba.

Ga cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu El-Hikaya.

Your browser doesn’t support HTML5

Bankin Masana'antun Najeriya Tace Ba Zata Yafe Bashin Naira Biliyan 3.4