Bankin Duniya Na Shirin Farfado Da Ilmin Yara A Jihar Bauchi

Bankin Duniya

Bankin Duniya ya kaddamar da shirin farfado da matsayin ilmin yara da ya lalace a jihar Bauchi, a sanadiyar rashin kai yara makaranta domin samun ilmi, wanda a halin yanzu bincike ya nuna cewar akwai yara da basa zuwa makaranta su fiye da miliyan 1 a jihar.

A matakin farko domin cimma manufar shirin, Bankin Duniyar ya zabo malamai gogaggu su 60, domin koya musu wasu dabarun cusa ilimi, wanda za suje makarantu domin su koyar da malaman makarantu dake yankunan kananan hukumomin jihar.

Hukumar samar da ilmi ta kasa a matakin jiha ita ce ke sa ido wajen tafiyar da wannan shirin.

Sai dai kuma matsalar ta karu da rashin kai yara makaranta da iyaye basa yi domin rashin abin hannu, da kuma sakaci. Amma wakilin Muryar Amurka ya tuntubi Malam Nuru Ahmed Daraktan tsare tsare a hukumar samar da ilmi na jiha, domin jin matakan da ake dauka da hukunci don magance matsalar.

Ga rahoto a sauti daga wakilin Muryar Amurka Abdulwahab Muhammad.

Your browser doesn’t support HTML5

Bankin Duniya Na Shirin Farfado Da Ilmin Yara A Jihar Bauchi