Dubban daruruwan Musulmi masu son zaman lafiya da neman farfado da bin shika-shikan addinin Islama sun yi wani taron yin sallar jam’i a jiya lahadi a kusa da Dhaka babban birnin kasar Bangladesh, a ranar kammala matakin farko na Sallolin jam’in kwanaki ukkun da ake yi shekara-shekara.
Ba a san adadin Musulmin da su ka halarci sallar karshen ba, wadda wani Limamin New Delhi, kasar Indiya ya yi minti ishirin ya na jagoranta. Amma wadanda su ka shirya taron sun kiyasta cewa Sallolin kwanaki ukkun da aka yi a gabobin kogin Turag sun samu halartar mutane fiye da miliyan hudun da su ka hada da dubban daruruwan bakin da su ka yi tattaki daga kasashen waje.
Tun shekarar 1966 Musulmin duniya sun ka fara yin taron yin Sallolin jam’i, da babu gamin shi da siyasa, wanda kuma ake kira Biswa Ijtema.
Frayim Ministar kasar Bangladesh Sheikh Hasina tare da sauran shugabanni sun bi Sallar jam’in daga kan rufin wani ginin gwamnati.
Masu shirya taron sun ce ranar 28 ga watan nan na Janairu za a yi wani taron kwanaki ukku na yin Sallolin jam’i a wurin da aka yi na wannan karo, domin a bada dama ga sauran su samu falalar irin wannan taro. Su ka ce an shirya taron yin Sallolin jam’in na biyu domin a gujewa cunkoson jama’a a taron na farko.