Bangarorin da ke fada a Sudan sun rattaba hannu a kan wata yarjejeniya da yammacin ranar Alhamis ta bada damar kai agajin jinkai, amma ba su amince su tsagaita wuta a rikicin da suke yi ba, a cewar wasu jami'an Amurka.
Wakilan sojojin kasar da na dakarun RSF, wadanda suka kwashe kusan wata guda suna fada, sun sanya hannu kan yarjejeniyar kare farar hular Sudan ne a birnin Jeddah na kasar Saudiyya, a cewar wani jami'in Amurka da ke cikin masu tattaunawar.
"Mun amince kan cewa muradin al'ummar Sudan da kare lafiyarsu sune abinda muka fi ba fifiko, kuma mun kuduri aniyar tabbatar da cewa an kare farar hula a kowane lokaci, abinda wakilan babban hafsan sojan kasar Abdel Fattah al-Burhan da na kwamandan rundunar RSF Mohamed Hamdan Dagalo suka fada wa kamfanin dillancin labaran AFP kenan.
"Yarjejeniyar ta kunshi ba farar hula damar barin wuraren da ake tashin hankalin sosai bisa son ransu, ta hanyar da suka zaba," a cewar sanarwar.
Yarjejeniyar ta kuma bukaci bangarorin biyu su bada damar kai agajin jinkai, su bari a maido da wutar lantarki, ruwa da sauran ababen more rayuwa, su kuma bari a janye jami'an tsaro daga asibitoci tare da bada dama a yi jana’izar wadanda suka mutu a mutunce.
A ranar Alhamis, da kyar hukumar kare hakkokin bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta zartar da wani kudiri na kara sa ido kan take hakkokin bil’adama a Sudan, inda aka kashe daruruwan farar hula tun bayan barkewar rikicin a watan Afirilu.