Masu sauraronmu assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa a wannan shirin na amsoshin tambayoyinku.
TAMBAYA 1: Ko me ya kawo rikicin kasar Sudan? Shin ta yaya za a magance yawan rikice-rikice a kasar?
MAI TAMBAYAR: Mainasara Nasarawa Funtua:
TAMBAYA 2: Assalamu Alaikum VOA Hausa don Allah ku tambaya Mana masana muhalli - dalilan fari, wato bushewar gonaki, a wasu kasashen da ke yankin Kuryar Africa, da ma wasu yakuna na kasar China dake yankin Asiya? A lokacin da wasu kasashen duniya suke fama da ambaliyar ruwa
MAI TAMBAYAR: Malam Aminu Adamu Mallam Madori, jihar Jigawa, Najeriya.
AMSOSHI : Ga amsar tambaya kan dalilan rikicin Sudan wanda wakilinmu a shiyyar Adamawa, Muhd Salisu Lado, ya samo daga wurin Dr. Mahdi Abba na Jami’ar Modibbo Adama da ke Yola, Adamawa Najeriya.
Ga kuma amsar tambaya kan musabbabin fari (bushewar gonaki) a wasu wurare, wanda wakilinmu a shiyyar Agadez, Janhuriyra Nijar, Hamid Mahmud ya samo daga masanin harkar yanayi da ke birnin Agadez, Malam Abubakar Nufi’u.
A sha bayani lafiya: