WASHINGTON D.C —
A shirinmu na bana bakwa,i a yau mun leka majalisar Nuhu Gandu ne inda muka ji irin nasu sabbin kalamomin da matasa ke anfani da su.
Sun fara da kalmar Shawaraki ko Gara wanda hakan ke nufin mutum wawa ne ko bashi da gane zance
Ko a ce Solawa wato ana nufin an jirga mutum ko an manta da shi, har ila yau matasan kan yi amfani da kalmomi irin su Shanyar da akayi ta bushe, ma'ana idan ka je wajen wani ka aika a kira makashi a cikin gida kuma ya dauki dogon lokaci sai wannan matashi ya sake aika wa don tunatar da wanda a ke jira da sakon cewar shanyar da yayi ta bushe .....
ku biyo mu domin wasu sabbin kalaman matasa a dDandalinvoa.com