A jawabinsa ga gwamnonin jihohin Najeriya, Ban Ki-Moon ya bayyana cewa za a gabatar da sabon tsarin mako mai zuwa a birnin New York na Amurka. Ya kuma yi kira ga gwamnonin su yi amfani da manufofin muradu masu dorewar su zama kinshikin gudanar da ayyukansu na gwamnati.
Babban Magatakardar ya bayyana cewa, shugabannin kasashen duniya zasu halarci taron koli mako mai zuwa a inda zasu tattauna kafin amincewa da tsarin muradu masu dorewar da za a aiwatar na tsawon shekaru goma sha biyar, wanda ya maye gurbin muradun karni da aka aiwatar cikin shekaru biyar.
Mr Ban Ki-Moon ya bayyana cewa, da yana ganawa da shugabannin kasashe ne, sai dai yanzu ya yanke shawarar ganawa da gwamnoni domin sune suke aiwatar da muradun kai tsaye, Yace Majalisar Dinkin Duniya a shirye take ta samar da wannan tallafin domin amfanin al’umma a wannan lokaci da yace muhimmi ne wajen yiwa ayyuka garambawul a Najeriya.
A cikin bayanansu, wadansu gwamnonin sun bayyana cewa, shirin muradun karni bai yi nasara ba sabili da ba a bishi sau da kafa kamar yadda aka tsara ba, inda ake gina dakunan shan magani ba tare da kayan aiki da ma’aikatan jinya ba, suka kuma bayyana matakan da suka fara dauka na yin gyara domin ganin nasarar sabon shirin.
Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Nasiru Adamu el-Hikaya ya aiki daga birnin tarayya Abuja, Najeriya
Your browser doesn’t support HTML5