Bamu da Hannu a Batun Cire Ibeto daga Sunayen Ministoci - Gwamnatin Neja

Ginin majalisun tarayyar Najeriya inda ake tantance sunayen ministoci da yanzu babu sunan Ahmed Ibeto ciki

Gwamnatin jihar Neja ta fito fili tace bata da hannu a batun cire Alhaji Ahmed Ibeto daga sunayen ministocin da shugaban kasa Muhammad Buhari ya mikawa majalisar dattawa domin tantancewa.

Ba zato ba tsammani shugaban majalisar dattawan Najeriya Sanata Bukola Saraki ya fitar da wata sanarwa daga shugaban kasa inda ya bayyana cire sunan Alhaji Ahmed Ibeto na jihar Neja daga sunayen ministocin da zasu tantance.

Dr. Ibrahim Doba kakakin gwamnan jihar Neja yace gwamnatin jihar bata ce a cire sunan kowa ba.

Kodayake babu wani cikakken bayani daga fadar shugaban kasa dan majalisar wakilan Najeriya daga jihar Neja Abubakar Lado Suleja yace yana ganin maganar mutunta bangare bangare ne ya kawo hakan.

Wakilin yace manyan shugabannin gwamnatin jihar, wato gwamnan jihar da sakataren gwamnati daga bangare daya suka fito da shi Ibeto. Tunda aka ambaci sunansa mutanen bangaren gabashin jihar suka fara korafi suna cewa an dannesu.

To amma na hannun daman Alhaji Ibeto Alhaji Isa Adamu yace sun bar wa Allah komi amma maganar mutunta bangare bangare ba dalili ba ne.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Bamu da Hannu a Batun Cire Ibeto daga Sunayen Ministoci - Gwamnatin Neja - 3' 06"