Bakinsu Yazo Daya Game da Tabbatar da Gaskiya da Adalci

'Yan gudun Hijira

Hadakar kungoyin sa kai dana fararen hula sun daura damarar sanya ido akan yadda za’a yi amfani da kudade da kayayyakin tallafi daga Gwamnatoci, kungiyoyi da hukumomi a ciki da wajen Najeriya domin farfado da rayuwar mutanen da hare-haren Bako Haram ya tagayyara a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Koda yake kungiyoyin na rajin bunkasa rayuwar jama’a, a fannoni daban daban ne amma bakinsu yazo daya game da batun tabbatar da gaskiya da adalci kan sha’anin farfadowa tare da sake gina rayuwar alumar lardun arewa ta gabas inda hare haren Boko Haram ya yiwa muguwar illa.

Hadakar kungiyoyin guda goma sun fito ne daga jihohin Borno da Yobe da Adamawa da Bauchi da Kano da Taraba da kuma jihar Gombe, a taron da kungiyoyin suka yi a Kano.

Kabiru Saidu Dakata na cibiyar fasahar sadarwa da ci gaba ya fayace manufarsu dagane da yadda yakamata a sarrafa tallafin.

Malama Halima Laminu, ta kungiyar “Network for civil society” daga jihar Yobe ta bukaci a baiwa fannin ilimi kaso mafi tsoka domin a cewar ta komai na rayuwa yanzu saida ilimi,idan an dauki kudin aka bayar babu ilimi tafiyarda kudin sais u salwanta, amma idan aka fara ingata ilimi saura abubuwan zasu daidaita.