Bakin Haure Sama Da Mutane 6000 Su Ka Mutu A Nahiyar Afrika

Bakin hauren suna wannan tafiya mai hadari ta cikin sahara na kokarin su na ketarwa zuwa kasashen turai domin samun ingantacciyar rayuwa.

Wasu sabbin bayanai daga hukumar kula da bakin haure ta kasa da kasa na cewa sama da ‘yan Afrika dubu shida suka mutu a tsakanin shekaru biyar, wanda galibinsu suna ratsawa a kan sahara zuwa Turai. Sai dai wannan adadi wani abu ne kadan a ciki abin da aka gano a wannan nazari.

A wannan shekarar kadai daruruwar mutane da suka shedi wannan al’amari sun tabbatar da mutane 1,400 suka mutu a nahiyar Afrika. Amma masu bincike sun ce wani abu ne kalilan a cikin babban adadi mutuwar mutane dake bulaguro a Afrika.

Hukumar bakin haure ta kasa da kasa ta fada cewa akasarin mutuwar suna faruwa ne a kan saharar Arewacin Jamhuriyar Niger da kudancin Libya da kuma Arewacin Sudan. Hukumar tace bakin hauren suna amfani da wadannan hanyoyi ne domin su isa kasar Libya wacce ta kasance kofar shiga nahiyar Turai domin samun abin kyautata rayuwa.

Mai magana da yawun hukumar kula da bakin haure Joel Millan yace masu fasa kwauri da masu safarar mutane ne ke amfani da hanyoyin da bakin hauren Afrikan ke bi kuma suna cutar da bakin hauren idan suka hadu dasu. Yace abubuwan da aka gano suna haddasa mutuwar bakin haure a Afrika za a iya magancesu.