Silivina Guedes bata jima da zama ‘yar kasar Amurka ba. A Mount Vernon, inda ya kasance tushen George Washington shugaban Amurka na farko aka yi bikin ta na shan rantsuwar zama ‘yar kasa.
Silivana ta ce “shekaru da dama ina rayuwa a nan, don haka me zai hana in zama ‘yar kasa kawai? Kuma hakan akayi.
Guedes ‘yar asalin kasar Portugal ce, sannan tana rayuwa sama da shekaru 20 a Amurka. Watan Nuwamban nan mai zuwa ne Guedes zata kada kuri’a a karon farko.
A cewar Guedes “Ina bibiyan al’amuran siyasa a kafafen radiyo da talabijin, sannan ina bibiyan muhawarorin da ake yi. Hakika, na bibiyi muhawarar karshe da aka yada ta tashar Univision (mai yada shirye-shiyen ta a harshen spaniyanci). A tunani na, yin hakan yana da mahimmanci don yana bani dama na fahimci alkiblar da 'yan takara suka dosa, manufofin su da kuma irin matakan da zasu dauka.”
Sannan masana sun ce bakin haure sabbin zama 'yan kasa da suka cancanci kada kuri’a zasu iya sauya akalar sakamakon zaben shugaban kasar da za ayi nan da 'yan kwanaki a watan Nuwamba, musamman ma a manyan jihohin raba gardama.
Mutanen da suka zama ‘yan kasa sama da dubu dari shidda (600,000) ne suke zama a Georgia, bisa bayanan shirin Rock the Naturalized Vote Project. Sama da dubu dari 400,000 a jihar Michigan, sannan akalla mutum dubu dari-hudu-da-sittin- da-biyar (465,000) a jihar Arizona.
Manuel Pastor shine na’ibin jagoran shirin a jami’ar South Carlifornia:
Ya ce “A jiha irin Arizona, mutanen da suka zama ‘yan kasa a tsakanin shekaru 8 zuwa 9 da suka shige sun kunshi kaso 2% cikin dari na mutanen da zasu kada kuri’a. Sannan, a jihar Arizona, a 2020, ratar da aka samu da ya kai ga nasara a jihar dan kalilan ne.”
A fadin Amurka baki daya, anyi kiyasin cewa mutum miliyan 3.5 ne da suka cancanci kada kuri'a suka zama ‘yan kasa tun daga zaben 2020, bisa kungiyar National Partnership for New Americans.