Bahasin Da James Comey Ya Bayar Gaban 'Yan Majalisar Dattijai

Daraktan hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka-FBI da aka kora James Comey, ya ce shugaba Donald Trump, ya nemi ya yi mishi biyayya, ya kuma bukaceshi ya daina binciken da ake gudanarwa kan tsohon mai bada shawarwari kan harkokin tsaro Micheal Flynn.

Comey ya shaidawa ‘yan majalisa cewa, bayanan da shugaba Trump da mukarrabansa suka bayar kan dalilin korarsa sun daure mashi kai

Gwamnatin ta zabi bata min da kuma, musamman hukumar hukumar FBI suna cewa, hukumar tana cikin rudani, kuma wai, bata da shugabancin kwarai, kuma ma’aikatan basu da kwarin guiwa kan shugabanta. Dukan wannan karya ce. Kuma nayi nadama ganin cewa, an shantalawa Amurka karya.

Comey yace, ranar goma sha hudu ga watan Fabrairu Trump yace mashi yayi watsi da binciken Flynn da ake gudanarwa. An kori Flynn da kwana daya a lokacin, sabili da shantalawa mataimakin shugaban kasa Mike Pence karya da ya yi, dangane da tattaunawarsa da jakaden kasar Rasha.


Comey yace shugaba Trump bai umarceshi ya dakatar da binciken Flynn dangane da alakarsa da Rash aba, sai dai yace, Na dauki abinda ya fada da wannan manufa.