Bada Tallafin Gwamnati Ga Dalibai Ya Rage Kalubalen Karatu A Da - Binta Abdulhamid

Hajiya Binta Abdulhamid

A yau dandalinvoa ya bakunci alewa irin ta da, wato ya sami zantawa da Hajiya Binta Abdulhamid, malamar makaranta wacce ta taka muhimmayar rawa a fannin ilimi a jihar Kano ta kuma bamu labarin yadda suka sami damar karatu a da da irin gwagwarmayar da suka fuskanta a rayuwa.

Ta fara da muhimmin batun cewa a wancan lokacin akwai wani Dr Usman malami da ke baiwa mata shawarar abinda ya kamata a matsayin mace ta karanta, wato fannin ilimi ko koyarwa saboda a wannan lokaci mafi yawan shugabanin makarantu ba ‘yan asalin jihar Kano bane.

Ko da yake ta ce ta canza ra’ayi bayan wannan shawara da malamin ya bayar inda a ranta ta fi burin ta karanci aikin jarida, ko da yake a wani lokaci na rayuwarta ta nemi aikin jaridar inda ta samu take tunanin zata cika burinta amma mai gida bai bada damar yin hakan ba.

Hajiya Binta, ta ce bata fuskanci wani kalubale ba a harkar neman ilimi domin a wannan lokaci babu wata matsala daga wajen iyaye da kuma gwamnati tunda a wancan lokacin gwamnati na taimakwa dalibai, kalubalen da ba’a rasa ba dai shine na hada karatu da aure tare da matsalar nisa daga gidajen dalibai da zuwa makaranta.

Ta ce a yanzu ba kamar da ba ne mata na iyakacin kokari wajen tura ‘ya’yansu mata makaranta domin su sami ilimi na zamani akalla zuwa sakandare kafin a yi mata aure.

Your browser doesn’t support HTML5

Bada Tallafin Gwamnati Ga Dalibai Ya Rage Kalubalen Karatu A Da - Binta Abdulhamid