Babu Wani Mai Cutar Ebola da Za'a Bari Ya Tafi Aikin Hajji

Alhazan da suka taru

Alhazan da suka taru

Jami'an kwastan da na shige da fice da ma'aikatan filayen jiragen sama sun bayyana irin matakan da gwamnatin tarayya ta dauka akan zuwa yin aikin hajjin bana a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Yola.

Batun da aka fi mayar da hankali akai bana shi ne batun cutar ebola, annobar da ta sa ma wasu kasashen yammacin Afirka ba zasu samu zuwa hajji ba bana.

Cutar ebola ta sa mahukuntan Najeriya sun sha alwashin zasu sa ido akan duk maniyattan kafin su samu su tsallake zuwa Saudiya. Alhaji Haliru Abdulrazak na hukumar kiwon lafiyar masu fita kasar yace bana ba zasu kyale duk wani alhajin da bashi da koshin lafiya ya tafi aikin hajji ba.

Akan cutar ebola Alhaji Abdulrazak yace binciken alhazan ya hada da ganin takardun da aka basu a asibitocin da suka yi gwaji. Idan sun iso filin jirgi za'a sake auna alhazan. Wanda yake da matsala tafiyarsa ta kare a nan.

Amma wani jami'in hukumar bada agaji ya bukaci hukumar alhazan jihar Adamawa ta dauki matakan kula da lafiyar maniyatta musamman a sansaninsu dake filin jirgin saman Yola. Maniyattan suna fuskantar matsaloli a wurin da aka tsugunar dasu na wucin gadi kafin su tashi. Yace wurin bashi da kyau. Ya nada kazanta ga kuma ciyawa. Maniyatta da ma masu kula dasu suna fama da zazzabi sabili da yanayin wurin. Yace ko gwamnati ta gyara wurin ko ta bada wani wurin da ya dace.

A jawabinsa shugaban tawagar alhazan jihar Adamawa mai martaba sarkin Mubi Alhaji Abubakar Isa Ahmadu ya saba layar bai mara da kunya ne kana ya bukaci maniyatta da su zama jakadu nagari. Yace aikin hajji daban yake da wasu ayyuka domin aikin ibada ce kuma sai mutum ya sadakar da ransa tun daga Najeriya zuwa Saudiya. Maniyatta su tabbatar sun bi kai'dodin tafiya.

Bana ana zaton maniyatta dubu hudu ne daga jihohin Adamawa da Taraba zasu sauke farali yayinda za'a fara jigilarsu daga filin jirgin saman Dutse na jihar Jigawa.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Babu Wani Mai Cutar Ebola da Za'a Bari Ya Tafi Aikin Hajji - 2' 51"