An samu rudani akan ko wata tawagar kwararru daga kasashen Duniya ta isa Birnin Douma da ke Syria, domin tantance ko an yi amfani da makamai masu guba a wani hari da aka kai akan garin, kwanaki 10 da suka gabata.
Kafar Talbijin din kasar ta Syria, da kungiyar ba da agaji ta “Red Helmet” kowannensu, ya ba da sanarwar cewar, tawagar kwararrun daga hukumar nan mai haramta yin amfani da makamai masu guba ta OPCW, ta isa Birnin na Douma.
Sai dai Mai Magana da yawun Ma’aikatar harkokin wajen Amurka, Heather Nauert, ta ce kwararrun ba su shiga garin ba.
Amma Jakadan Syria a Majalisar Dinkin Duniya, Bashar Jaafari, ya fadawa kwamitin tsaro na majalisar cewa, tawagar ta samu shiga Douman a jiya Talata.
A dai ranar Asabar, wato ranar da Amurka da Birtaniya da Faransa suka kai hari akan Syria, kwararrun hukumar ta OPCW suka isa kasar ta Syria.
Sai dai da farko ba a basu damar danganawa da Birnin na Douma ba, wanda ke kusa da Damascus, babban Birnin Syria, a yunkurin da suke yi na kokarin gano ko an kai hari da makamai masu guba a ranar bakwai ga watan nan na Afrilu.
Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta ce, lura da cewa an samu tsaikon kwanaki goma da kai harin, mai yiwuwa ba za a ga shaidar da ke nuna cewa an yi amfani da makaman masu guba ba, idan aka yi la’akkari da cewa Rasha da dakarun Syria ne ke rike da yankin, inda shugaba Emmanuel Macron na Faransa ke nanata cewa Rasha na da hanu dumu-dumu a harin.
ACT 1”Lallai, Rasha na da hannu, na fadi hakan, kuma na fadawa shugaba Putin da safe, ba wai da kansu suka yi amfani da sinadarin Chlorine mai guba ba, sun dai yi wani siddabaru ne na hana kasashen Duniya dakile amfani da makaman masu guba.”