Mai magana da yawun gwamnati, Josh Earnest, ya ce hukumar bincike ta FBI na ci gaba da bincike kan wannan kutse, yana mai cewa akwai sauran aiki a gaba kafin a tantance inda matsalar ta ke.
Da farko hukumomin tsaron kasar sun ce masu kutse daga China ne suka aikata wannan laifi wadanda ake tsammanin suna da alaka da gwamnatin kasar ta China.
Sai dai hukumar ta FBI ba ta bayyana yadda ta kaiga wannan matsaya na ganewa cewa China c eke da alhakin kutsen ba.
A yau Juma’a, Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar China, Hong Lei, ya yi fatali da wanna zargi lamarin da ya kwatanta a matsayin abin da bas hi da tushe, yana kai cewa ire-iren wadannan kutse ana gudanar da su ta ko’ina ba kuma da wuya a gane ko wake da alhakin yin kutsen.
Ofishin kula ma’aikatan kasar Amurka, y ace akalla ma’aikata miliyan hudu abin ya shafa wadanda suka hada da ma’aikata na yanzu da wadanda suka bar aiki.
Wannan kutse ana mai kallon mafi girma akan ma’aikatun gwamnati da aka gani a cikin ‘yan shekarun nan.