Babu Sansanin Sojin Ketare A Najeriya – Shelkwatar Tsaro

Daraktan Yada Labaran Ma'aikatar Tsaron, Manjo Janar Edward Buba

Manjo Janar Buba ya bukaci al’umma su yi watsi da labarai da rade-radin da ake yadawa a wasu kafafe.

Shelkwatar tsaron Najeriya ta musanta rahotannin dake cewa rundunar sojin Faransa na shirin kafa sansani a Najeriya.

Sanarwar da daraktan yada labaran shelkwatar tsaron, Manjo Janar Edward Buba ya fitar a yau Litinin ta ce karin hasken ya zamo wajibi sakamakon rahotannin da ake yadawa, na cewa sojojin Faransa sun riga sun sauka a kasar.

“An ja hankalin shelkwatar tsaro game da rahotannin yanar gizo dake zargi game da isowar ayarin farko dakarun Faransa a birnin Maiduguri da nufin kafa sansanin soajan Faransa a shiyar arewa maso gabashin Najeriya.

“Da kakkausar murya rundunar sojin Najeriya ke sanar da cewar babu kamshin gaskiya a wannan labari kuma ba komai illa tsagwaron karya da makirci.

Manjo Janar Buba ya bukaci al’umma su yi watsi da labarai da rade-radin da ake yadawa a wasu kafafe.