Umar Unguwa Uku wanda aka fi sani da "Umar UK" ya ce da dama mutane na yi wa mawaka wani irin kallo na mutane ne da suke koyar da dabi’ar da bata dace ba a cikin alumma.
Umar ya ce duk wani mawaki na fuskantar kalubalen kalon mai isar da sakonni ta hanyar da bata dace ba, kuma akan haka ne ma ya ke mayar da hankali wajen fitar da wakokin da zai nusar da al'umma dangane da wannan sana’a ta su.
Ya kara da cewa da harkar ta waka ne yake isar da sakonnin fadakarwa, wa’azantarwa da ma nishadantarwa, domin a wayar da kansu dangane da yadda ya kamata su tafiyantar da rayuwarsu.
Ya ce a yanzu dabi’ar shaye shaye da zamantakewa a hannu guda kuma a nishadantar da masu sauraro, yace al'ummar mu ta dauke wata tarbiya da ba ta malam Bahaushe ba ta ara ta yafa.
Daga karshe ya ce da harkar wakar ne yake fadakarwa tare da fayyace wa al'umma abinda basu gane ba ko ya shige masu dubu.
Your browser doesn’t support HTML5