Gwamnan jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya Seyi Makinde ya musanta ikirarin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi cewa ya ba jihohin kasar naira biliyan 570.
A wani jawabi da ya yi wa ‘yan Najeriya a ranar Lahadi don kwantar da kurar zanga-zangar da aka yi kan tsadar rayuwa, Tinubu ya yi ikirarin bai wa kowace jihar kasar naira biliyan 570.
Sai dai Makinde wanda dan jam’iyyar adawa ta PDP ne, ya ce babu gaskiya a kalaman na Tinubu.
“Gwamnatin tarayya ba ta ba wata jiha kudi ba; kudadenmu ne da muka kashe aka biya mu, an yi amfani ne kawai da gwamnatin tarayya aka turo da kudin ta hannunta.
A cewar Makinde, kudaden an maido musu ne kan shirin farfadowa daga annobar COVID-19 da Bankin Duniya ya ce su aiwatar, wanda ka’idar ita ce, kowace jiha sai ta fara amfani da kudinta kafin bankin na duniya ya mayar mata.
“Da farko an ba mu naira biliyan 5.98, a karo na biyu kuma aka ba mu naira miliyan 822.” Makinde ya ce cikin wata wasika da ya wallafa a shafinsa na X.
Wasikar ta Makinde amsa ce ga neman karin haske da wani dan jihar ya yi game da abin da gwamnatin Oyo ta yi da kudaden da Tinubu ya ce ya ba jihohi 36.
“Saboda haka, bari na fada muku kai-tsaye cewa ikirarin da gwamnatin tarayya ta yi akwai kuskure a ciki.
“Yana da muhimmanci a fahimci cewa, kudaden bashi ne ba tallafi ba ne.” Makinde ya ce.