Daya daga cikin matasan arewa da suka baiwa ‘yan kabilar Igbo, wa’adin cewa su tattara inasu inasu su bar arewacin Najeriya, yace bai fahimci abinda suke nufi a wannan daftari da suka rattabawa hannu a Kaduna ba.
Shugaban kungiyar rajin kawo canji a arewa “Arewa Citizens Action For Change” Sharif Ashir, yace babu inda suka ce ayi tashin hankali, illa sun fadi matsayin kungiyar kuma suna da ‘yacin fadi matsayin su a Najeriya.
Yana mai cewaya kyautu Gwamnatin Najeriya ta yiwa ‘yan kabilar Igbo rafarada ma’ana taron yaba gardama domin akwai dokar ta majalisar dinkin duniya da ta amince da idan mutane suka ce suna son ‘yancin kansu a basu.
A yayin da yake maida martini aka lamarin wani basaraken gargajiya ma zaunin Abuja, Eze Maxwell Kanu, yace shima yana goyon bayan ayi kuri’ar raba gardama. Yace dole ne su bii bukatun nasu da lalama da kuma yin aiki tukuru na neman hadin kai a daidai lokacin da ake begen ayi kuri’ar raba gardaman ta haka ne zamu san bukatun juna ba a mulki dole.
Your browser doesn’t support HTML5