Hukumomin da ke shirya bikin ba da kyautar gwarzon dan kwallon duniya ta Ballon d’Or, sun ce ba za’a sami damar gudanar da bikin na wannan shekara ta 2020 ba, haka kuma ba za’a bayyana gwarzon shekarar ba.
Hukumar kwallon kasar Faransa ce ke daukar nauyin ba da kyautar a kowace shekara, to amma ta ce a bana ba za’a sami gudanar da ba da lambar yabon ba karon farko tun da aka soma a shekarar 1956, sakamakon annobar coronavirus da ta wargaza tsarin zaben gwarzon dan kwallo da sauran rukunoni daban-daban da ake zaben gwaraza.
Lionel Messi na kungiyar Barcelona da Cristiano Ronaldo sun mamaye kyautar a baya-bayan nan. Messi ya lashe lambar yabon sau 6, yayin da Ronaldo kuma ya sami lambar sau 5.
Hukumar ta ce ta dage gudanarda bikin ne saboda rashin tsarin takara da zaben fitattun ‘yan wasa bisa adalci da kamanta gaskiya kamar yadda aka saba, sakamakon yadda annobar ta coronavirus ta hargitsa al’amura.