Babu Gudu Babu Ja da Baya A Yaki da Cin Hanci da Rashawa - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na kara kaimi a kan yaki da cin hanci da rashawa, yace babu gudu babu ja da baya kuma babu sani babu sabo har sai ya ga bayan almundahana da munamuna a kasar.

Yayinda yake yiwa ma'aikatan fadarsa jawabi, wadanda suka taru su yi mashi maraba da dawowa daga Ingila inda ya je neman jinya, Shugaba Buhari ya sake tabbatar masu cewa zai cigaba da yiwa kasar jagoranci da duk iyakacin karfinsa da adalci tare da dukufa wajen ganin ya inganta rayuwar talakawan kasar.

"A duk rayuwata ban taba yadda da cin hanci da rashawa ba. Idan mun yi kuskure cikin abubuwan da mu keyi kana muka yi watsi da adalci, kasar zata kara komawa baya", inji Muhammad Buhari.

Shugaban ya cigaba da cewa "ba zamu taba duk wanda bai taba dukiyar jama'a ba. Idan ka yiwa kanka kiyaumar laini zaka samu barci mai lafiya, 'ya'yanka da iyalanka zasu dinga samun girmamawa daga jama'a"

"Amma idan ka yi rub da ciki da dukiyar jama'a za'a kama ka a gurfanar da akai gaban kotu", inji shugaban.

Daga karshe Shugaba Buhari ya godewa ma'aikatan fadar gwamnati saboda kyakyawan aikin da suke yiwa kasar ya kuma gargadesu su kasance masu kishin kasa tare da gujewa cin hanci da rashawa yayinda suke aikinsu.

Yace "ina fada maku ku sake sadakar da kanku wa kasarku. Kamar yadda na fada shekaru talatin da suka gabata bamu da wata kasa in ba Najeriya ba. Mun kuduri aniyarsake gina kasar nan wa 'ya'yanmu da jikokinmu da ma na biye dasu"

"Matakan kawo canji basu da sauki, amma idan mun dukufa da gasken gaske zamu ci nasara mu shawo kan duk matsalolin da muke fuskanta yanzu", inji shugaban.