Babu Dokar Neman Daidaita Raba Gado Tsakanin Maza da Mata a Majalisar Dattawa-Ndume

Sanata Ali Mohammed Ndume

Makon jiya wani dan majalisa Olujimi aka ce ya gabatar da wani kudurin kawo daidaito akan rabon gado tsakanin maza da mata lamarin da ya sa malaman addinin musulunci suka yi dari dari da kudurin tare da neman 'yan majalisa suyi watsi dashi.

Damuwar da malaman addinin musulunci suka nuna ya sa 'yan majalisar dattawa daga arewa fitowa su ce babu wani kuduri makamancin hakan a gabansu.

'Yan majalisar sun fahimtar da mutane cewa babu wani dalilin dogon korafi.Haka ma Sanata Ali Ndume yace babu wani kuduri makamancin hakan a gabansu baicin yunkurin wasu 'yan majalisar na neman gyaran al'adu.

Baicin cewa babu kudurin gabansu, Sanata Ali Ndume yace majalisar dattawa bata da hurumin kafa wata dokar da ta shafi addinin wani domin kundun tsarin mulkin kasa ya fada babu dokar da za'a yi da zata shafi addinin kowa. Ya kira jama'a kada kowa ya tada hankalinsa.

Shi ma Sanata Kabiru Gaya yace kodayake kudurin ya kaiga karatu na biyu idan ya dawo ba zai kaiga koina ba saboda ya sabawa addinin musulunci da al'adar jama'a. Hatta wadanda ma ba musulmi ba ya karya al'adarsu. Yace babu yadda zasu bari kudurin zama doka har yayi tasiri.Yace ranar da aka dawo da kudurin don karatun karshe ranar zai mutu.

Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Babu Dokar Neman Daidaita Raba Gado Tsakanin Maza da Mata a Majalisar Dattawa-Ndume - 3' 35"