Jami'an sun ce tattaunawar da ake a Astana babban birnin kasar Kazakhstan, wadda kasashen Rasha da Turkiyya ke daukar nauyinta, ba ta kai tsaye ba ce, bangarorin biyu na tattaunawa da juna ne ta wajen masu shiga tsakanin.
Tattaunawar da ake yi a birnin Astana ta fi mai da hankali ne kan yadda za a jaddada yarjajjeniyar tsagaita wuta ta kasa baki daya, wadda Rasha da Iran da Turkiyya suka taimaka aka cimma a watan Disamban bara, yarjajjeniyar da aka kiyaye a akasarin wurare cikin kasar ta Siriya.
Tattaunawar zaman lafiyar Siriya da aka yi a lokuta daban-daban a can baya, ciki har da ta baya-bayan nan da aka yi bara, ba su kawo wani cigaba na a zo a gani ba wajen kawo karshen tashin hankalin da aka fara tun watan Maris na shekarar 2011.