A dai dai lokacin da ‘yan Najeriya, ke jiran ranar ashirin da daya (21) ga wannan wata ranar da mukaddashin shugaban kasa zai zauna da wakilan jama’a daban daban domin warware matsalar fafutukar neman Biafra, da kuma wa’adin da matasan arewa suka baiwa al’umar Igbo, na komawa yakinsu.
A yanzu rukunin jama’a daban daban sun far bada shawarar hanyoyin da ake ganin cewa za a bi domin samun maslaha kan wannan matsala da Najeriya ke ciki a yanzu.
Farfesa Ango Abdullahi, daya daga cikin dattawan arewa wanda ake fatar suyi Magana da matasan domin janye wannan wa’adin da kuma daina yin wani barazana na tada zaune tsaye a cikin kasar ya bayyana hanyoyin da yake ganin zai kyautu abi domin samun daidaito.
Ya ce sai manyan kabilar Igbo sun fito “sun ce abinda suke yi ba daidai bane abinda ‘ya’yan su suke yi ba daiadai bane” jama’a sun ji alokacin ne za a fahimci cewa da gaske suke.
Wani matashi dan kabilar Igbo, Godwin Ogene,ya ce batun rabuwa ba zai yu ba saboda an dade ana tare kuma zaman tarayya yafi dadi kowane bangare na bukatar a zauna lafiya.
Mukaddashin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya kammala tattaunawa da tuntuba da yake bukatar yi domin samun matsayi guda da zai gabatarwa dattawa da manyan da zasu halarci taron da za a gudanar a ranar ashirin da daya (21) ga wata domin tsara daftarin da za a bi domin samun tabbatatciyar zaman lafiya tsakanin ‘yan Najeriya.
Your browser doesn’t support HTML5