Kungiyar lauyoyi masu rajin demokaradiyya a Najeriya wato Lawyers for Sustainable Democracy in Nigeria, ita ce ta shigar da karar a makon jiya, tana mai ikirin cewa majalisar ta karya sassan kundin tsarin mulki tare da yin azababi wajen daukar gabarin wannan aiki na bincikar zargin rashawar dala miliyan biyar daga hannun ‘yan kwamgila.
Zaman kotun na ranar Litini karkashin jagorancin Justice A.T Badamasi ya ta’allaka ne a kan tababar fassarar umurni da kotun ta bayar ne wadda ke hani ga majalisar ta dakatar da binciken zuewa lokacin sauraron shari’ar.
Ita dai majalisar a baya tace odar kotun ba ta fito karara ta hana aikin binciken ba, a don haka bata fahimtar cewa, a dakatar da aikin binciken faifen bidiyon.
Alkalin kotun mai shari’a AT Badamasi ya nanata bukatar dakatar da binciken har sai kotun ta kammala sauraron gundarin shari’ar.
To amma a yayin tafka mahawara, lauyan majalisar dokokin Barriter Mohammed Waziri ya fadawa kotu cewa, dama kwamitin bai ci gaba da aikin binciken ba.
Barriter Muhammed Zubair dake zaman shugaban kungiyar lauyoyin data gurfanar da majalisar gaban kotun ya bayyana jin dadinsa a kan yanda ba a samu jayayya a kan karar da suka shigarwa kotun a kan dakatar da binciken.
Ga dai cikakken rahoton da wakilin mu a Kano Mahmud Ibrahim Kwari ya aiko mana:
Your browser doesn’t support HTML5