Da yake yanke hukunci a safiyar Litinin, Mai Shari’a James Omotoso ya ce kasafin da gwamnan ya gabatar a gaban mambobi hudu na majalisar da ke tsaginsa, haramtacce ne.
Kotun ta kuma tabbatar da karar da Majalisar da Kakakin Majalisar Martin Amaewhule suka shigar kan Fubara, wanda ya nemi a ba shi umarnin hana Gwamnan cikas a Majalisar a karkashin jagorancinsa a matsayinsa na Kakakin da sauransu.
Don haka ya umarci gwamnan ya sake gabatar da kasafin a gaban halastaccen zauren majalisar karkashin jagorancin Martin Amaewhule, daga tsagin tsohon gwamnan jihar kuma ministan Abuja, Nyesom Wike.
Rikicin Wike da Fubara ya raba kan majalisar dokokin jihar, inda akasarin mambobin suke bangaren Wike suka kuma sauya sheka zuwa APC, har suka tsige sohon shugaban majalisar suka nada daya daga cikinsu.
Gwamnan ya rike kudaden majalisar sannan ya sauya wa magatakardan majalisan da mataimakinsa wurin aiki, a matsayin martinsa kan baren ’yan bangaren Wike.
Amma alkalin ya sanar cewa gwamnan ba shi da hurumin hana majalisar dokokin jihar kudadenta.
Daga nan ya yi wa gwamnan gargadi game da yunkurin kawo cikas ko yin katsalanda ga harkokin gudanar da majalisar da Amaewhule ke jagoranta.
Alkalin ya kuma soke sauyin wurin aiki da gwamnan ya yi wa magatakardan majalisan da mataimakinsa.
Haka zalika ya umarci Sufeto-Janar na 'yan Sandan Najeriya ya ba da isasshen tsaro ga shugaban majalisar da mambobin majalisar da ke adawa da gwamnan.