Babbar kotu a jihar Bauchi karkashin mai shari'a Mua’zu Abubakar ta hana duk wani bincike da majalisar wakilai ta keyi game da rikicin shugabancin majalisar dokokin jihar Bauchi.
Kotun ta kuma hana kakakin majalisar tarayyar da kwamitin da aka kafa don bin diddigin rikicin, duk wasu masu neman rikicin, dasu guji sa hannu a wannan al'amarin domin komai yana gaban kotun shara’a
Za a iya tunawa rikicin majalisar dokokin jihar Bauchin ya farune a sanadiyar zaben da ya gudana inda aka samu kakakin majalisa guda biyu, don hakan ya zamana tilas majalisar wakilai ta tarayyar, ta kafa kwamitin gano matsalar a karkashin shugabancin Honorabul Sarki Adar.
Lauyan masu shigar da kara Barista Jibrin Sa'id Jibrin yayi karin haske game da hukuncin kotun, inda yace an sabawa doka, dalilin zuwa kotu ke nan don neman hukunci.
Shima da yake bayani mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Bauchin Danlami Ahmed Kawule, yayi bayanin matsayin majalisar dokokin. Yace majalisar tana yin komai dai-dia, shiya sa dole a jira kotu da bada hukunci.
Gamayyar hadin gwiwar kungiyoyin siyasa a jihar Bauchin ta bayyana matsayinta kan rikicin majalisar. Honorabul Sani Ahmed Burra wanda shine shugaba, yace suna nuna goyon bayan su, domin anbi kaidar yadda ya kamata. Kuma za'a samu daidaitawa ba tare da wasu sun sa hannu a ciki ba.
Abdulwahab Muhammad ya hada wannan rahoton.
Your browser doesn’t support HTML5