Babbar Cibiyar Islama Ta Goyi Bayan Yaki Da Polio

Ana ba yaro maganin cutar Polio

Cibiyar Fiqhu ta Kasa da Kasa ta bayyana goyon bayanta ga gudanar da aikin rigakafin, tana mai cewa ta fitar da Fatawa kan wannan.
Cibiyar Fiqhu ta Kasa da Kasa ta bayyana goyon bayanta ga gudanar da aikin rigakafin cutar shan inna a Najeriya, tana mai fadin cewa ta fitar da Fatwa ta yin tur da duk wani mutumi ko gungun mutanen da suke gudanar da aikin yin rigakafin cutar Polio a cikin Najeriya.

Har ila yau, kungiyar ta yi kira ga iyaye da su tabbatar da cewa an yi ma ‘ya’yansu maza da mata rigakafin wannan cuta ta Polio.

Cibiyar Fiqhum, wadda bangare ce ta Kungiyar Kasashen Musulmin Duniya, OIC, ta ce tana mai yin tur da kai farmaki a kan masu gudanar da aikin yin rigakafin.

Kungiyar ta ce ya zamo wajibi ga iyaye su kyale ayi ma ‘ya’yansu rigakafin wannan cuta.

Goyon bayan da wannan cibiya take bayarwa ya biyo bayan wani taron da aka kira na manyan malaman addinin Musulunci a Jami’ar al-Azhar dake al-Qahira, babban birnin Masar.

A Najeriya dai, Sarkin Musulmi, Sultan Sa’ad Abubakar na Uku, shi ne ke jagorancin kawar da cutar Polio a cikin kasa.

A lokuta da dama, Sultan ya roki niyaye da su kyale a diga ma ‘ya’yansu maganin rigakafin wannan cuta ta Polio, yana mai jaddada cewa babu wata illa tattare da ita.
Sarkin Musulmi yace an gudanar da bincike sosai a kan wannan maganin rigakafin cutar Polio, kuma an gano cewar ba ta tattare da wata illa ko kadan.