Idan aka duba yadda kasashen duniya suka damu matuka bisa ga matsalar tafkin Chadi, hakane yasa don sanin yadda girman matsalar take ne muka tuntubi ‘Dan Masanin Fika Alhaji Bababa Abba, wanda yake tsohon babban sakatare ne a hukumar raya tafkin Chadi.
‘Dan Masanin Fika, ya bayyana mana cewa a yadda gurin yake tabbas ya ragu, domin za a iya cewa yanzu haka gurin na ‘daya bisa gomar yadda yake a baya. Haka kuma idan har aka mayar da tafkin yadda yake a baya to lalle ba Najeriya kadai zai taimakawa ba har ma da makwabtanta wanda suka hada Nijar da Chadi da Kamaru.
Shi kuma farfesa Alasan na Jami’ar Abuja, cewa yayi akwai kogi masu yawa da suka hadu da tafkin Chadi, amma yanzu haka an datse su anyi Dam akan su, kogin Jama’are ne kawai ya rage to ruwan da ke shiga takfkin Chadi ya ragu wanda har ya janyo wa manoma da masu sana’o’i matsala.
Mataimakin Darakta a ma’aikatar Muhallin Najeriya Mr. Ben Benigun, yace tun farkon hawan shugaba Buhari mulki ya fara yunkuri akan tafkin Chadi. In yace ma’aikatar ruwa na aiki tukuru inda har ta mikawa shugaban kasa wani daftari, yanda za a yi a jawo ruwa daga sauran wurare ya zuwa tafkin Chadi.
Saurari rahotan Wakilin Muryar Amurka Hassan Maina Kaina.
Your browser doesn’t support HTML5