Wadanda suka nuna shugabannin jam'iyyar sunyi kokarin taimakawa Madam Hillary Clinton, ta wajen yin ba'a ko kaskantar da abokin takararta Bernie Sanders.
Magajiyar gari na birnin Baltimore, Stephanie Rawlings-Blake, wacce har ila yau itace sakatariyar kwamitin jam'iyyar Democrat ta kasa, itace ta bude4 taron jiya Litinin a madadin Shugabar jam'iyyar ta kasa Debbie Wasserman Schultz.
An ture Wasserman daga kan wannan mukami, bayan da dandalin tsegumi ko fallasa da ake kira Wikileaks ya kwarmato emails kusan dubu 20, da jam'iyyar tayi zargin Rasha ta sato watannin baya.
Kamin a bude taron gadan gadan, Senata Sanders yayi kira ga magoya bayansa su goyi bayan Hillary Clinton, ya nuna bukatar a hada kai domin su tunkari dan takarar jam'iyyar Republican Donald Trump.Amma magoya bayansa suka yi masa ihu lokacinda ya bukaci a goyi bayanta.
Daf da za'a fara babban taron, uwar jam'iyyar ta Democrat ta fitar d a sanarwa ta nemi gafara daga Senata Sanders da magoya bayansa, "saboda munanan kalamai da aka yi akansa cikin rubuce rubucen email din." Jam'iyyar tace rubuce rubucen basu nuna halayenta ko manufofi da jam'iyyar ta dogara akansu da kuma kasancewa ta kowa tsakanin masu takara karkashin inuwar jam'iyyar.